Kayode Egbetokun, Ya Isa Benue, Tare Da Runduna Ta Musamman Don Dakile Kisan Gilla

Babban Sufeton Rundunar ‘Yan Sanda na Ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya isa jihar Benue a ranar Litinin, domin  yin duba da irin halin da ake ciki sakamakon hare-haren da ake ci gaba da kaiwa al’ummar jihar wanda ya yi musu illa, inda aka kashe daruruwan mutane tare da raba da dama da muhallansu.

Ziyarar ta Babban Sufeton na zuwa ne bayan barkewar wani sabon rikici a jihar, inda wasu ‘yan bindiga suka kai mummunan hari a kan al’ummomi da dama a ranar Juma’a da ta gabata.

Rahotanni na cewa kimanin mutane 160 ne suka rasa rayukansu a harin, wanda ake kallon sa a matsayin daya daga cikin mafi muni da jihar ta fuskanta a ‘yan shekarun nan.

Jihar Benue, wadda ke da matuƙar muhimmanci wajen samar da abinci a yankin Arewa ta Tsakiya, na fama da rikice-rikicen da ake alakantawa da sabani tsakanin manoma da makiyaya.

Sai dai a ‘yan makonnin da suka gabata, rikicin ya ɗauki sabon salo, inda ake samun rahotannin hare-hare da kashe-kashe kusan kullum.

Majiyoyi sun bayyana cewa ziyarar ta Babban Sufeton na cikin wani babban mataki na tsaro da ya haɗa da tura ƙarin jami’an rundunoni na musamman domin tallafawa ‘yan sandan da ke jihar wajen dakile hare-haren da tabbatar da maido da zaman lafiya.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da kisan gillar, inda ya bukaci hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa.

A cewar Shugaban kasar a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi “Kashe-kashen da ke faruwa a jihar Benue na da matuƙar tayar da hankali. Dole ne mu kawo ƙarshen wannan zubar da jini. kuma ya isa haka,”.

“Ina umartar jami’an tsaro da su dauki mataki ba tare da jinkiri ba, su cafke duk masu hannu a wannan ta’asa daga kowanne ɓangare, tare da gurfanar da su a gaban kuliya.”

Da Isar Babban Sufetonm  jihar, al’ummar Benue na cike da fatan ganin an dauki matakan gaggawa da samar da sakamako  da nufin  dakile wannan matsala.

Previous Post Next Post