Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, sun yi tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan kasar Girka, Kyriakos Mitsotakis, ranar Lahadi domin tattauna yadda rikicin da ke kara kamari tsakanin Isra’ila da Iran ke ci gaba da dagula yankin, A cewar kamfanin dillancin Saudiyya.
A cewar rahoton, shugabannin biyu sun yi nazari kan halin da ake ciki a yankin, tare da mayar da hankali kan illar da harin sojojin Isra’ila ke haddasawa ga Iran.Sun jaddada bukatar daukar matakin hakuri da kauce wa ci gaba da rikicin, tare da nanata muhimmancin amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen warware sabani, in ji rahotan.
Wannan tattaunawa ta biyo bayan yadda rikicin da ke faruwa tsakanin kasashen biyu, inda kowanne bangare ke kai wa juna hare-hare na martani.
Masana da shugabannin duniya na nuna fargabar rikicin na iya sauya akala zuwa wani babban rikici a yankin, inda ake ci gaba da bukatar kowa ya mayar da takobi cikin kube.