Tinubu Na Aiki Tukuru Don Shawo Kan Matsalolin Ƙasa

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Dakta Barau Jibrin, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu,  na aiki tukuru domin magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.

Sanata Barau ya bayyana hakan ne a garinsa na Kabo, Jihar Kano, bayan kammala sallar Eid al-Adha, inda ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji matsalolin tattalin arzikin da ke cikin mawuyacin hali tare da ƙalubalen tsaro masu tsanani.

“Shugaban ƙasa na jajircewa wajen tabbatar da cewa matsalolin da suka addabi ƙasar nan za sun zama tarihi a cikin kankanin lokaci.

 Amma wannan na buƙatar haɗin gwiwar kowa da kowa da kuma addu’ar ‘yan ƙasa,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan gwamnati da yin addu’a don samun nasara da zaman lafiya.

Sanata Barau ya kuma taya al’ummar Musulmi murnar bikin Eid al-Adha, inda ya buƙaci su yi amfani da lokacin wajen yin tunani, taimakon juna, da kuma addu’ar samun shiriya da jagoranci mai kyau ga shugabanni na ƙasa

Previous Post Next Post