Majalisa Ta Wanke Kasar Togo Daga Bada Digirin Bogi

Majalisar Wakilan Najeriya ta wanke ƙasar Togo daga zargin  bayar da takardun shaidar kammala karatu na bogi, inda a halin yanzu zargin kacokan ya koma kan Jamhuriyar Benin, inda aka gano shaidu dake nuna yadda  ake cinikin  takardun kammala  karatu a matakai daban daban .


Shugaban Kwamitin Majalisar kan Ƙorafe-ƙorafen Jama’a, Honarabul Bitrus Laori, ne ya bayyana haka a birnin tarayya  Abuja, bayan wani korafi da wani  kamfanin lauyoyi na Sovereign Legal Practitioners ya shigar a madadin manyan masu ruwa da tsaki a fannin ilimi na kasar.

Ƙarar ta kalubalanci hukuncin da Ma’aikatar Ilimi ta  gwamnatin Tarayya ta yanke a bara, wanda ta haɗa ƙasashen Togo da Benin a cikin zargin bada shaidar kammala digiri  na bogi, wanda  hakan ya  yamutsa  hazo a kasar nan.

Laori ya bayyana cewa binciken diflomasiyya da Ma’aikatar Harkokin Waje ta gudanar ya tabbatar da cewa Togo ba ta da hannu a cikin lamarin, tare da ƙara jaddada ingancin cibiyoyin iliminta.

Kwamitin ya sanya ranar 10 ga watan Yulin 2025, domin ci gaba da sauraren korafin, inda a halin yanzu  zata  mayar da hankali  kan Jamhuriyar Benin kadai.

Previous Post Next Post