Kotun Afirka ta Kudu ta bude sabon bincike kan kisan gillar da aka yi shekaru 40 da suka gabata

 

Kotun Afirka ta Kudu ta bude sabon bincike kan kisan gillar da aka yi shekaru 40 da suka gabata na masu fafutukar kawar da tsarin wariyar launin fata guda hudu da wasu jami’an yansanda  suka yi.

Babu wanda aka gurfanar a gaban shari’a game da kisan gillar da aka yi wa mutanen guda hudu a  shekarar 1985, kuma iyalansu sun zargi gwamnati da yin katsalandan don hana ruwa  gudu a  shari’ar.



Malaman makarantar da aka halaka su uku, sun hada da  Fort Calata sai  Matthew Goniwe da Sicelo Mhlauli, tare da wani  ma’aikacin jirgin kasa Sparrow Mkonto,  inda aka sace su tare da  kashe yayin da suke komawa gida daga wani taron siyasa a garin Cradock da ke kudancin kasar.

Wannan shi ne binciken shari’a na uku game da kisan mutanen guda hudu wanda ya faru ne a lokacin da gwamnatin masu mulkin mallaka  ke tsananta wa masu fafutukar kawar da launin fata.

Previous Post Next Post