Hukumomin kasar Saudiyya sun
hana fiye da mutane dubu 269, da ba su da izinin zama a kasar a hukumance
shiga birnin Makkah kafin fara
aikin hajjin bana.
Wannan mataki, kamar yadda
jaridar Al Arabiya ta ruwaito a ranar Lahadi, na cikin wani yunkuri na rage
cunkoson jama’a da tabbatar da tsaro yayin aikin hajji na wannan shekara.
Ma’aikatar Cikin gida ta kasa ta bayyana cewa wannan matakin yana shafar baki da mazauna Saudiyya da ke kokarin yin hajji ba tare da samun izini ba.
An kuma saka tara
ta kimanin dala dubu
5, ga wadanda aka samu da aikata
lefin, tare da yiwuwar korar su
daga cikin kasar. Bugu da kari hukumomin kasar sun
hukunta sama da mazauna kasar dubu
23,000 saboda karya dokokin hajji sannan an soke lasisin masu bada
ayyukan hajji guda 400.
A wani taron manema labarai
da aka yi a Makkah, Janar Mohammed al-Omari ya bayyana wa ‘yan jarida cewa,
bisa ka’ida, Iya wadanda ke da izinin yin hajji ne aka yarda su gudanar da
aikin, ko da suna zaune a birnin makkatun mukarrama.