Hukumar kula da yanayi ta
kasa NiMet ta yi hasashen za a samu guguwar iska da ruwan sama daga Litinin
zuwa Laraba a jihohin Kano, Taraba, Kaduna, Gombe, Bauchi, Kebbi, Sokoto,
Katsina da Jigawa.
NiMet ta bayyana hakan ne a
cikin rahoton yanayi da ta fitar a ranar Lahadi a Abuja, inda ta yi hasashen
yiwuwar samun guguwar iska da ruwa a wasu sassan jihohin Taraba, Kaduna,
Sokoto, Borno, Kebbi da Zamfara daga baya a ranar.
Hukumar ta kuma yi hasashen
za a samu guguwar iska da ruwan sama da safe a ranar Talata a wasu sassan Kano,
Zamfara, Katsina, Bauchi, Gombe, Adamawa, Borno, Yobe da Taraba.
Tags:
Labarai