Mutanen da ke kusa da sansanin Soji na Giwa, sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta sauya matsugunin sansanin daga cikin gari.

 Mutanen da ke kusa da sansanin Soji na Giwa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta sauya matsugunin sansanin daga cikin gari.

Mutanen sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a Maiduguri, inda suka nuna damuwarsu kan haɗarin da suke fuskanta kasancewar su a kusa da cibiyar ajiye kayayyaki soji da'yan ta'addar da aka kama.



Wannan buƙata ta biyo bayan fashewar wani abu a dakin ajiyar makamai na sansanin Giwa a watannin baya, wanda ya haddasa lalacewar wasu makaman yaki da wasu gine-gine da ke kusa da sansanin.

Shugaban kungiyar Zauren Tattaunawa na Galtimari, Zannah Boguma, ya bayyana cewa sansanin Giwa na ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan Boko Haram da ke kokarin kubutar da abokansu daga gidan da sojoji ke ajiya da su.

Previous Post Next Post