NDLEA, ta ƙaddamar da wani gagarumin samame a Dorayi, Gwammanja, Zango da Ja’en, inda ta cafke mutane 19 a Kano.
Samame na daga cikin wani yunkuri da hukumar ke yi na kawo karshen maboyar masu shan miyagun ƙwayoyi da wuraren taruwar masu aikata laifuka.
NDLEA ta bayyana cewa yawaitar shaye-shaye ne ke haddasa ƙaruwar aikata laifuka, musamman tada hankali da rashin zaman lafiya.
Kakakin hukumar ya ce wannan aiki ya nuna jajircewar kwamandan rundunar NDLEA ta Kano, CN A I Ahmad, wajen dakile safarar miyagun kwayoyi da kuma samar da tsaro ta hanyar magance musabbabin aikata laifuka tun daga tushe.
An kwace miyagun kwayoyi daban-daban a yayin samamen, tare da kama wadanda ake zargi da hannu a lamarin. Wannan na daga cikin matakan da hukumar ke ɗauka domin kare rayukan al’umma da inganta zaman lafiya.
Hukumar ta bukaci hadin kan al’umma wajen ci gaba da bayar da sahihan bayanai da kuma kai rahoton duk wani abu da ake zargi, domin tabbatar da nasarar yaki da safarar kwayoyi da aikata laifuka a fadin jihar Kano.