Masarautar Gaya Ta Tuɓe Rawanin Sarautar Wazirin Gaya Daga Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji

 Majalisar Masarautar Gaya da ke cikin Karamar Hukumar Gaya ta tuɓe rawanin  sarautar Wazirin Gaya daga hannun tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji.


Sanarwar tuɓe rawanin
 sarautar ya fito ne a yau ta bakin Sakataren Masarautar Gaya, Alhaji Bello Halilu, wanda ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne saboda wasu dalilai da ba a iya kauce musu ba.

Alhaji Bello ya bayyana cewa matakin ya nuna yadda masarautar ke dagewa wajen kare mutunci, kima da martabar sarautun gargajiya bisa tsarin al'adu da dabi'u da aka gada.

Wannan mataki na zuwa ne kasa da mako guda bayan da wata kungiyar siyasa mai suna APC Patriotic Volunteers karkashin jagorancin Alhaji Usman Alhaji, ta soki yadda Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ke tafiyar da mulkinsa.

Previous Post Next Post