Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Katsina ta yi nasarar dakile wani yunkurin sace mutane, tare da ceto mutane hudu da suka hada da Mata uku da wata jaririya a kauyen Mazare, da ke karamar hukumar Sabuwa ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba, 18 ga Yuni, 2025.
A cewarsa: “Da misalin karfe 12:21 na dare, ofishin ‘yan sanda na Sabuwa ya samu kiran gaggawa kan wani hari da ‘yan bindiga suka kai kauyen Mazare, inda suka harbe mutane biyu – Sa’idu Isa mai shekaru 37 da Sa’idu Wa’alam mai shekaru 61 – kafin yin garkuwa da mutane hudu.”
Aliyu ya ce, nan take jami’an ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin DPO suka Isa wajen da abin ya faru. A yayin musayar wuta tsakanin su da 'yan bindiga, tasa ‘yan bindigar suka tsere sakamakon shan 'barin wutar da suka fuskanta daga hannun jami’an tsaro.
https://www.krmhausa.com/2025/06/yan-sanda-sun-kama-mutane-biyu-kan.html
https://www.krmhausa.com/2025/06/yan-sanda-sun-cafke-mutum-182-kaduna.html
Ya tabbatar da cewa an ceto dukkan wadanda aka yi garkuwa dasu cikin koshin lafiya, ba tare da wani rauni ba. Yayin da wadanda suka ji rauni a harin an garzaya da su asibiti, inda aka bayyana cewa suna samun sauki.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Bello Shehu, ya yaba da jaruntaka da ƙwarewar jami’an da suka halarci aikin ceton.
CP Shehu ya jaddada kudurin rundunar na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar, yana mai kira ga al'umma da su ci gaba da ba ‘yan sanda hadin kai ta hanyar bayar da bayanai a kan duk wani motsi ko abin da basu aminta da shi ba.
Ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin kama ‘yan bindigar da suka tsere, yayin da bincike ke gudana a kan harin.