Rundunar ‘Yan Sanda a jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar wani tsohon jami’in sojan Najeriya mai murabus, Major Joe Ajayi, wanda ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane duk da biyan kudin fansa har naira miliyan 10 da iyalansa suka yi domin a sako shi.
Kakakin rundunar, DSP Williams Ovye-Aya, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ranar Litinin a Lokoja.NAN ta ruwaito cewa an sace Major Ajayi, mai shekaru 76, a gidansa da ke Odo-Ape a karamar hukumar Kabba-Bunu ranar 21 ga watan Mayu.
DSP Ovye-Aya ya bayyana cewa an samu gawar mamacin kuma ta dakin ajiyar gawa na Asibitin Kwalejin Kabba, kamar yadda kungiyar dattawan Bunu ta tabbatar. Ya kara da cewa rundunar 'yan sanda za ta yi bakin kokarinta wajen cafke wadanda suka aikata wannan danyen aiki domin su fuskanci fushin doka.
Haka zalika, Shugaban kungiyar dattawan Bunu, Farfesa Olu Obafemi, tare da sakatarensa, Ade Abanida, sun tabbatar da faruwar lamarin. Sun bayyana cewa masu garkuwar sun fara bukatar fansa na naira miliyan 50, amma iyalan basu iya biyan kudin ba.
Hakan ya sa lafiyar tsohon sojan ta kara tabarbarewa sakamakon rashin magani.
"Masu garkuwar daga baya sun saukar da bukatar kudin fansar zuwa naira miliyan 10 bayan sun lura da cewa yana cikin halin rashin lafiya sosai,".
"Iyalansa sun amince da bukatar ne da fatan za su samu damar ceto rayuwarsa, amma abin takaici, bayan biyan kudin, da aka ce a je a dauke shi, sai dai aka tarar da gawarsa."
A nasa bangaren, Sanatan da ke wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, Sunday Karimi, ya bayyana wannan mummunan lamari a matsayin abin bakin ciki da takaici.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a Lokoja, Sanata Karimi ya koka da yadda tsaro ke tabarbarewa a yankin, yana mai cewa yankin Kogi ta Yamma gaba daya na fama da hare-haren masu garkuwa da mutane,
inda al’umma ke cikin fargaba da tsoro,