Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta bayyana cewa, wani samame da rundunar Operation Hadin Kai ta gudanar ya lalata muhimmin sansanin horar da ‘yan ta’adda da ke Bukar Meram, a kudancin tafkin Chadi, jihar Borno.
A cewarsa, samamen da aka gudanar a ranar Litinin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da suka samu na wasu shirye-shiryen ‘yan ta’adda na kai farmaki a garuruwan Marte da Monguno.
Ejodame ya kara da cewa “Harin jiragen sama ya yi sanadin hallaka da dama daga cikin ‘yan ta’addan, tare da lalata kayayyakin da suke yaki da su, da suka hada da motocin daukar kaya, wuraren adana makamai da mafakan da suka kera Makamai,”.
Ya ce bayanan da ke fitowa daga binciken barnar da aka yi musu, sun tabbatar da cewa an dakile barazanar farmakin da ‘yan ta’addan ke shirin kaiwa yankunan Marte da Monguno.
“Rundunar sojin saman Nijeriya [NAF] na ci gaba da dagewa wajen kare fararen hula da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa, musamman a yankin Arewa maso Gabas da ma fadin kasar nan,” in ji Ejodame.