Sojojin Sun Kashe 'Yan Ta’adda 10 a Kudancin Tafkin Chadi

Rundunar Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar Sojojin Task Force ta  hadin gwiwa (MNJTF) sun kashe ‘yan ta’adda 10 a yayin wani artabu da suka yi a yankin Rann–Gamboru Ngala, wanda ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.



Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne yayin wani samame da sojojin ke gudanarwa domin kakkaɓe ragowar ‘yan ta’adda da ke fakewa a cikin al’ummomin kan iyaka.

Rahotanni na cewa sojojin sun yi arangama da ‘yan ta’addan ne a wata maboyar su  tsakanin Rann da Gamboru, lamarin da ya janyo musayar wuta. Sojojin sun samu nasarar fatattakar su tare da kashe 10 daga cikinsu.

An kwato tarin makamai da harsasai daga wajen ‘yan ta’addan, ciki har da harsasan bindigar harbo jirgin sama, wadanda hukumomin leken asiri ke zargin cewa sun ɗauke su ne daga wani hari da ‘yan ta’addan suka kai wa Sojojin Kamaru a baya.

“Wannan samamen wani bangare ne na kakkaɓe 'yan ta'addan a yankin kudancin tafkin Chadi domin hana su zirga-zirga tsakanin kasashe,” in ji wata majiya daga jami’an tsaro.


Previous Post Next Post