Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kama mutum 182 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, tare da kwato makamai, harsasai da kuma miyagun kwayoyi, a wani gagarumin samame da undunar ke ci gaba da gudanarwa a fadin jihar.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce samamen an gudanar da shi tsakanin ranakun 9 zuwa 13 ga watan Yuni, a wuraren da aka fi zargin ayyukan masu laifi kamar Rigasa, Kawo, Tudun Wada da Sabon Tasha.DSP Hassan ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Rabiu Muhammad, ne ya bayar da umarnin gudanar da wannan samame domin karfafa kwarin gwiwar tsakanin al'umma da magance matsalolin rashin tsaro.
A cewar sanarwar, jami’an ‘yan sanda sun sami nasarar kwato buhuna 30 dauke da daurin wani ganye 1,600 da ake zargin tabar wiwi ce, tare da wasu makamai masu hadari.
Sanarwar ta kara da cewa "Ranar 13 ga Yuni, 2025, jami’anmu sun kai samame yankin Rigasa, inda suka kwato kwayoyi da k ganyen wiwi. Haka kuma, a yayin wani artabu da masu laifi a Rafin Guza, an ga wani wuri da aka sami bindigar AK-47 mai dauke da harsasai 3, wadanda ake zargi suka arce sun bar ta,".
A wani cigaba na bincike, DSP Hassan ya ce jami'an ‘yan sanda daga sashin Kakuri sun kama wani mai Ziya'u Abdullah mai shekara 35, da laifin yunkurin siyar da mota da ake zargin ta sata ce. Bincike ya kai ga cafke wani da ake zargi abokin aikinsa ne, mai suna Bashir Usman da aka fi sani da "Yellow".
"Yayin gudanar da tambayoyi ga wadanda ake zargi, sun amsa laifin kai hari wani gida a unguwar Gona, inda suka yi amfani da wukake da adda suka kwace mota kirar Honda Accord, wacce daga bisani aka gano ta Zaria,".
Rundunar ta bayyana cewa wasu daga cikin wadanda ake zargin tuni an gurfanar da su a gaban kotu, yayin da ake ci gaba da bincike kan sauran, kuma za a gurfanar da su da zarar an kammala bincike.