Hukumar tace fina-finai da Ɗab'i ta Jahar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba El-mustapha ta bayyana shirinta na saka ƙafar wando ɗaya da duk wani gidan wasa da ɗakunan taro ko masu kiɗan DJ da a ka samu da aikata yin rashin da a a yayin gudanar da bikin sallah a Jahar Kano.
Hukumar ta kafa wani kwamiti na musamman da zasu kewaya gidajen wasannin tare da dakunan taro a ranakun Babbar sallah ƙarƙashin kulawar Alh. lawan Hamisu Dan Hassan Daraktan da ke lura da sashin fina-finai na hukumar.
Kwamitin wanda aikinsa shine saka ido a kan dukkannin gidajen wasannin da ɗakunan taro a Jahar Kano, hadi da masu kidan DJ zai tabbatar ba aa bawa masu shigar banza ko shaye - shaye damar shiga gidajen wasannin ko dakin taro dama ba, haka kuma, Hukumar ta hana hada maza da mata a guri ɗaya a yayin bikin na babbar sallar.
Abba El-mustapha, yace kwamitin zai rinka aiki ne dare da rana kuma cikin sirri da a bayyane tun daga ranar daya ga babbar sallah har zuwa lokacin da za'a kammala bikin sallar domin cimma nasarar aikin da aka sa a gaba.
Abba El-mustapha ya yi gargadi da kakkausar murya ga masu gidajen wasanni da dakunan taro tare da masu sana'ar DJ dasu bi dokokin hukumar sau da kafa domin gujewa fushin doka.
A karshe ya yi kira da iyaye dasu cigaba da kula da tarbiyar 'ya'yansu tare da addu'ar Allah yasa ayi bikin na sallah lafiya a gama lafiya