Tinubu Ya Yi Kira Ga Hadin Kan ‘Yan Najeriya, Da Ya Yi Sojoji Addu’a

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai don gina Ƙasa da nufin yin alfahari da ita, yana mai jaddada bukatar zaman lafiya da kulawa da juna a lokacin bukukuwan Sallah.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne bayan kammala sallar Eid-el-Kabir a filin salla na Dodan Barracks da ke Legas, a ranar Juma’a. Ya bukaci jama’a da su ci gaba da yi wa dakarun kasar addu’a, wadanda ke bakin kokarin su wajen yaki da ta’addanci da tabbatar da tsaron kasa.

“Dole ne mu sadaukar da kai, mu tuna da addu’a da kuma taimaka wa masu karamin karfi. Don tabbatar da zaman lafiya, ya kamata mu hada kai, mu zama masu kulawa da juna, mu taimaki makwabta kuma mu nuna soyayya ga kowa ba tare da la’akari da bambance-bambancen mu ba,” in ji shugaban kasa.

Ya jinjinawa sojojin Najeriya bisa sadaukarwar da suke yi domin kare kasar daga kalubalen tsaro, yana mai bukatar a yi addu’a ta musamman a gare su.

“Dole ne mu yi addu’a mai karfi a gare su, mu tuna da sadaukarwar su, tare da girmama su, kuma mu kasance masu halayen kirki.”

Previous Post Next Post