Tawagar Ceto ta Kudu Afrika Na Cigaba da Neman Sauran Masu Rai, Bayan Ambaliya Ta Halaka Mutum 49

A ranar Alhamis, tawagogin ceto a Kasar Afrika ta Kudu na ta kokarin kai dauki ga wadanda ambaliya ta shafa a lardin gabas na kasar, inda aka tabbatar da mutuwar akalla mutane 49.

Ruwan sama mai karfi tare da guguwa mai tsanani sun rutsa  yankin Gabashin Cape — wanda yanki ne na masu kananan karfi sosai, kuma mafi yawan jama’arsa manoma ne — tun daga ranar Litinin. Ambaliyar ta yi sanadin rushe gidaje tare da tafiya da wata motar makaranta da ke dauke da yara, hudu daga cikinsu har yanzu ba a gan su ba.


Mai magana da yawun gwamnatin lardin, Khuselwa Rantjie, ta bayyana cewa akwai yiyuwar mutane da dama har yanzu ba a san inda suke ba. Ta kara da cewa akalla tawaga kungiyoyi biyar ne ke gudanar da aikin ceto a yankin birnin Mthatha, kimanin kilomita 800 (ko mil 500) kudu da Johannesburg.

Gwamnan lardin, Lubabalo Oscar Mabuyane, ya tabbatar da cewa daga cikin mutanen da suka mutu, hudu yara ne. Ya ce yaran suna cikin wata motar makaranta mai dauke da yara 11 da ambaliya ta tafi da ita. Hukumomi ta ce an tabbatar da mutuwar yaran hudu da manya biyu a cikin motar, yayin da yara uku suka tsira da ransu.

“Ba mu taba ganin irin wannan iftila'i na ruwan sama mai tsanani a lokacin sanyi irin haka ba,” in ji Mabuyane. 

Ta kara da cewa wani yaro ya rasu yayin da ruwa ya tafi da shi a hanyar zuwa makaranta.

Gwamnatin lardin ta ce sama da mutane 600 ne suka rasa matsuguninsu, inda da dama ke samun mafaka a dakunan taron jama'a. Hukumomi na cikin gida sun bayyana cewa an sami mummunan lalacewa ga gine-gine da ababen more rayuwa, ciki har da wutar lantarki da ruwan sha. Akalla cibiyoyin lafiya 20 ne ambaliyar ta shafa.

Cibiyar Nazarin halin rayuwa da kididdigar marasa karfi (Southern African Regional Poverty Network) ta bayyana cewa wannan yanki — inda tsohon shugaban kasar Nelson Mandela ya fito — na daga cikin mafi talauci a kasar, inda kashi 72 na al’umma ke rayuwa cikin talauci.

Shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa hukumomin bada agaji, ciki har da Cibiyar Kula da Bala’o’i ta Kasa, suna daukar matakan gaggawa domin rage radadin wannan iftila’i.

Previous Post Next Post