Gogaggiyar mai tsaron gidan Super Falcons, Chiamaka Nnadozie, ta kulla yarjejeniya da kulob din Mata na gasar Premier ta Ingila, Brighton & Hove Albion.
Kulob din Brighton, wanda ake kira The Seagulls, ya daukI Nnadozie, bayan kwantiraginta da Paris FC ya kusa karewa. Zata zama cikakkiyar ’yar wasa ta Brighton daga ranar 1 ga Yuli, lokacin da kwantiraginta a Faransa zai kare.
Brighton ta yi nasarar kan Everton wajen samun sa hannun tsohuwar mai tsaron gidan ta kungiyar kwallon kafar Rivers Angels.
Nnadozie ta kwashe shekaru biyar a Paris FC, inda ta taimaka wa kulob din ya lashe Coupe de Feminine a wasan karshe da suka doke Paris Saint-Germain, ta tsaya kyam inda ta ceci kungiyar a bugun fanareti guda biyu.
Tags:
Wasanni