Tinubu Zai Halarci Taron BRICS a Brazil

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Asabar, 28 ga Yuni, 2025, domin kai ziyara ta musamman  Saint Lucia da Brazil.



Ziyarar ta farko za ta fara ne a Saint Lucia, inda Shugaba Tinubu zai kai ziyara ta ban girma da karfafa dangantaka da kasashen yankin Caribbean.

A Saint Lucia, Shugaba Tinubu zai gana da Gwamna-Janar na kasar, Cyril Charles, da Firayim Minista Philip Pierre. 

Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi na musamman a zaman hadin gwiwar Majalisun Dattawa da Majalisar Wakilai na Saint Lucia, wanda za a gudanar a dakin taro na William Jefferson Clinton Ballroom, Sandals Grande, Gros Islet.

Daga nan ne Shugaba Tinubu zai zarce  birnin Rio de Janeiro na Brazil domin halartar Taro na 17 na kungiyar BRICS, inda zai hadu da sauran shugabannin kasashe mambobi domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban tattalin arziki da hadin kai.

Previous Post Next Post