Sojojin Sama Sun Tarwatsa ’Yan Ta’adda a Neja

Rundunar Sojojin Saman Najeriya (NAF) ta yi lugudan wuta kan 'yan ta'adda karkashin Operation FANSAN YAMMA Sector 1, inda ta kashe da dama tare da lalata maboyarsu a Jihar Neja.


Hare-haren, wadanda aka gudanar daga 24 zuwa 26 ga Watan Yuni, sun gudana ne tare da hadin gwiwar sojojin kasa da sauran jami’an tsaro, bayan samun sahihan bayanai game da ayyukan ’yan ta’addan a kauyukan Kakihun da Kumbashi.

Daraktan hulda da Jama’a na shelkwatar NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce an kai harin ne kan ’yan ta’addan da ke da hannu wajen kai hare-hare da kuma satar shanu a yankin.

Sanarwar ta kara da cewa, Mun samu bayanai na sirri, inda muka yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro, muka aika jiragen yaki cikin gaggawa. Mun kai luguden wuta tare da lalata maboyar ’yan ta’adda, da kashe da dama.

NAF ta bayyana cewa wannan aiki ya nuna  saurin kai ɗauki da ɗaukar mataki kan lokaci, tare da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin fararen hula.

Rundunar Sojin Sama ta tabbatar da kudurinta na ci gaba da goyon bayan kokarin gwamnati wajen dawo da zaman lafiya a fadin kasar nan.

Sanarwar ta ce Rundunar Sojin Sama za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya tare da yin aiki da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Previous Post Next Post