Mai tsaron ragar ƙasar Rasha,
Stanislav Agkatsev, ya bayyana kungiyar Super Eagles ta Najeriya a matsayin ɗaya
daga cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa mafi ƙarfi a duniya.
Rasha za ta kara da ƙungiyar super
eagles a wasan sada zumunta a ranar Juma’a a Filin wasa na Luzhniki da ke
Moscow.
Super Eagles na shigowa wasan
ne da ƙwazo bayan lashe gasar Unity Cup a birnin London. Ƙungiyar Eric Chelle
kuma ba ta yi rashin nasara a wasanninta huɗu da ta buga ba. 
Agkatsev ya ce yana da
matuƙar muhimmanci ga Rasha ta gwada ƙarfin ta da ƙungiya irinta Najeriya. Za’a
fara gudanar da wasan ne da misalin karfe 6 na yamma.
Tags:
Wasanni
