Rundunar sojin Najeriya ta kai wani gagarumin samame ta sama a wani sabon sansanin 'yan ta'addan ISWAP da ke dajin Baikee a yankin Gwoza, Jihar Borno. Rahotanni daga Jaridar PR Nigeria sun bayyana cewa an raunata daruruwan 'yan ta’adda, ciki har da shugaban su mai suna Abu Moussab al-Barnawi, wanda ya yi fice wajen kai hare-hare a yankin.
Wannan farmaki na jiragen yakin sama ya gudana ne a ranar 13 ga Yuni, a karkashin Operation KALACHEN WUTA, a wani farmaki na musamman da Operation Hadin Kai ke jagoranta don tarwatsa 'yan ta'adda a yankin dajin Izge–Pridang–Baikee.
Sojojin sun kai farmaki ne a daidai lokacin da 'yan ta’addan ke kokarin kafa sabon sansani don shirya kai hare-hare a garuruwan da ke yankin, musamman garin Izge. An bayyana cewa kwamandan rundunar, Manjo-Janar Abdulsalam Abubakar, ne ya jagoranci wannan aiki tare da Air Commodore UU Idris na sojin sama.
A jerin hare-haren da aka kai, an lalata kayayyakin aiki da dama wadanda ISWAP ke amfani da su. Rahoton Battle Damage Assessment (BDA) ya tabbatar da mummunar asara da ISWAP ta tafka, ciki har da raunukan da Abu Moussab al-Barnawi ya samu a fuska da hannayensa – lamarin da ya sanya babu tabbas kan ko zai iya ci gaba da jagorantar kungiyar.
Duk da yake rundunar sojin Najeriya na ci gaba da kokarin murkushe ayyukan ta’addanci a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, har yanzu 'yan ta’adda da masu garkuwa da mutane na ci gaba da samun hanyoyin kai hare-hare da aikata laifuka a yankunan.