Rundunar ‘Yan Sanda A Bayelsa Ta Tabbatar Da Sace Alkali a Yenagoa

Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Bayelsa ta tabbatar da sace Justice E.J. Umokoro, alkali a Babbar Kotun Jihar Bayelsa, da yammacin ranar Asabar a birnin Yenagoa, babban birnin jihar.



Mai magana da yawun rundunar, DSP Musa Mohammed, ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadi cewa: An Sace Alkali E.J. Umokoro  ne a yankin Ekeki na Yenagoa yayin da yake cikin motarsa a gaban wani wajen sayar da abinci.

Ya ce bayan samun rahoton, rundunar ta tura tawagogin kwararrun jami'an tsaro da kuma na’urorin tattara bayanan asiri na sama (drones) domin bin sahun masu garkuwar da nufin cafke su.

Rahotanni daga Kamfanin dillacin labarai na Kasa (NAN) sun bayyana cewa masu garkuwar sun zo dauke da bindigu, inda suka bude wuta a cikin filin ajiye motoci na wajen abincin, sannan suka tilasta wa alkali Umokoro fitowa daga motarsa.

An ce lokacin da lamarin ya faru, alkalin yana jiran diyarsa wadda ta shiga cikin wajen domin yin siyayya, kafin lamarin ya faru.

Jami’an tsaro na ci gaba da kokarin gano inda aka kai alkali Umokoro da kuma ceto shi cikin koshin lafiya.

Previous Post Next Post