Donald Trump, ya bayyana cewa dakarun sojin Amurka sun kaddamar da hare-haren da ya kira "babba nasarori” a kan muhimman cibiyoyin nukiliyar Iran da ke Fordow, Natanz da Isfahan.
A cikin jawabinsa, ya yi kashedi ga Iran da sauran abokan gaba cewa:
“Ku sani, akwai sauran manyan wuraren da muke iya kai hari idan aka kuskura aka kai hari na ramawa gayya.”
A martaninsa, Ministan Harkokin Wajen Iran ya soki hare-haren Amurka yana kiran su da “abinda bai dace ba,” tare da bayyana su a matsayin hare-hare kan shirin nukiliyar zaman lafiya na Iran.
Ya ce:
“Wannan hari ya haifar da illoli da za su dade ba su wuce ba.”
Abangare guda kuma, Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan yankunan tsakiyar da arewacin Isra’ila, wanda ya jikkata akalla mutane 23, bisa rahoton da ke fitowa daga hukumomin yankin.
Rahoton Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya (IAEA) ya tabbatar da cewa, har yanzu babu sinadarin radiyo da ya karu a waje da wuraren da aka kai hari a Iran — alamar cewa harin bai haddasa fitar sinadarai masu hadari ba.
A Isra’ila, Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya yaba da matakin Trump, yana mai cewa:
“Wannan mataki jarumta ne da Isra’ila da Amurka suka yi aiki kafada da kafada wajen yanke wannan shawara.”
Tun bayan da Isra’ila ta fara kai farmaki a ranar 13 ga Yuni, Iran ta bayyana cewa mutane fiye da 400 sun mutu, kuma fiye da 3,000 sun jikkata. A Israel kuwa, Iran ta kashe akalla mutane 24 ta hanyar mayar da martani.
Tashin hankali a Gabas ta Tsakiya na ci gaba da kara tsananta, inda kasashen duniya ke kira da a koma teburin sulhu domin dakile rikici mai yuwuwar rikidewa zuwa yakin duniya.