Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, Ya Soki Matakin Shugaba Trump Kan Iran

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya soki matakin da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya dauka na kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran, yana mai bayyana shi a matsayin “mataki mai hadari da zai kara dagula lamarin.”



Guterres ya bayyana damuwarsa cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, yana cewa:

“Nayi matukar damuwa da yadda Amurka ta yi amfani da karfi a kan Iran a yau. Wannan wani babban kalubale ne ga zaman lafiya da tsaron duniya a yankin da tuni ke kan halin yaki.”

Ya kara da cewa akwai barazanar cewa rigimar zata kara ta'azzara, lamarin da zai yi mummunan shafar fararen hula a yankin Gabas ta Tsakiya, da ma duniya gaba ɗaya.

Guterres ya bukaci kasashen duniya da su guji tayar da hankali da kuma mutunta dokokin da aka shimfida a ƙarƙashin tsarin Majalisar Dinkin Duniya da sauran dokokin kasa da kasa.

Ya kara da cewa “A wannan mawuyacin lokaci, wajibi ne a guji fadawa cikin rudani da rikici. Babu mafita wajen yin amfani da soja. Hanya daya tilo ita ce ta diflomasiyya. Fata daya tilo kuma shi ne zaman lafiya,”.

Kasashen duniya da dama sun fara mayar da martani da kira ga diflomasiyya da jan kunne kan barazanar rikici da ka iya zama mai girma.

Previous Post Next Post