Sojojin Najeriya Sun Kashe Kwamandan ISWAP Da Wasu ‘Yan Ta’adda Da Dama a Borno Da Yobe

Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe wani kwamandan kungiyar ISWAP mai suna Malam Jidda, tare da wasu mayaƙansa da dama a wani farmaki na haɗin gwiwa ta sama da ƙasa a karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe da yankin Timbuktu  na jihar Borno.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Reuben Kovangiya, mukaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin ƙasa, Shelkwatar Operation Hadin Kai, ya fitar a Maiduguri ranar Talata.

A cewar sanarwar, an kaddamar da wannan farmaki ne a ranar 9 ga Yuni a yankin Ngazalgana da ke karamar hukumar Gujba, tare da goyon bayan dakarun sojin sama na OPHK.

“An tabbatar da halaka Malam Jidda a  Ameer na ƙauyukan Ngorgore da Malumti, inda ya rasa ransa yayin wata musayar wuta tsanani da dakarun soji, inda suka fi karfin ‘yan ta’addan da makaman zamani,” inji sanarwar.

Sanarwar ta ce wasu daga cikin ‘yan ta’addan sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da wasu kuma suka rasa rayukansu a wani farmaki na bazata da aka kai a yankin Timbuktu.

Sanarwar ta ƙara da cewa “A yayin ci gaba da sintiri a yankin Mallamfatori na karamar hukumar Abadam, an gudanar da wasu hare-hare a baya-bayan nan, dakarun sun gano wasu gawarwakin ‘yan ta’adda da suka mutu, tare da kwato makamai da kayan aiki,”.

Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da: bindigogi kirar AK-47 da babura da  bututun harba rokoki da harsasai da dama da abubuwan fashewa da sauran kayan yaki.

Mai magana da yawun rundunar ya ce sabon farmakin yana nuna ƙwazon da OPHK ke ci gaba da nunawa wajen yaƙi da ‘yan ta’adda, musamman samun taimakon hare-haren jiragen yaki da aka tsara da kyau.

Ya sake jaddada kudirin rundunar sojin ƙasar nan na ganin an kawar da Boko Haram da ISWAP baki ɗaya tare da dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

Previous Post Next Post