Facebook Zai Goge Tsofaffin Bidiyon Kai Tsaye, Sakamakon Sauye-sauye a Shafin

Kamfanin Facebook ya sanar da cewa zai fara goge dukkan bidiyon Facebook kai tsaye (Live) da aka watsa sama da kwanaki 30 da suka gabata, a wani sabon tsarin adana bayanai da yake aiwatarwa.



Wannan na nufin duk bidiyon Facebook na kai tsaye (Live) da aka watsa kafin ranar 19 Ga Fabrairu, 2025, za a bada damar  sauke su har zuwa ranar 7 Ga Yuli. Bayan wannan lokacin, duk bidiyon da ba a sauke ba, kamfanin zai  goge daga shafuka da rumbum adana bayanan masu amfani da shafin da suka wallafa su.

Facebook ta shawarci masu shafuka, ciki har da shafukan kafafen yaɗa labarai,  da su ziyarci  (settings) na shafukan su domin duba  tsarin yadda za su sauke tsofaffin bidiyon su kafin ƙarshen wa’adin na 7 ga watan Yuli.

Previous Post Next Post