Wani Matashi Ya Rasu Sakamakon Faɗawa Rijiya

Wani Matashi  mai shekaru 33, Muhd Sagir, ya rasu sakamakon faɗawa cikin rijiya a unguwar Kawon Alhaji Sani, Layin Mai Unguwa, da ke karamar hukumar Nasarawa, a cewar hukumar kashe gobara ta jihar Kano.

Haɗarin ya faru ne da misalin karfe 12:42 na rana, inda hukumar ta samu kiran gaggawa daga mazauna yankin, tare da bayar da rahoton cewa wani mutum ya fadi cikin rijiya.

Darakta na hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Sani Anas, ya jagoranci tawagar ceto da suka isa wurin cikin gaggawa, inda suka ciro mutumin daga rijiyar cikin rashin hayyaci.

Sai dai duk da kokarin da aka yi, marigayin bai farfado ba, inda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.

Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya bayyana cewa an mika gawar marigayin ga dagacin Kawon Arewa, Alhaji Hamisu, domin daukar matakan da suka dace.

Hukumar ta bukaci jama'a da su kara kula da lafiyarsu da kuma tabbatar da rufe rijiyoyin da ba a amfani da su, domin kaucewa afkuwar irin wannan lamari mai tayar da hankali.

Previous Post Next Post