APC Na Neman Kwankwaso Ya Mara wa Tinubu Baya a Zaben 2027 — Sharada

Wani jigo a tafiyar Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Yusuf Sharada, ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki na ta ƙoƙarin jawo Kwankwaso domin ya goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.



Sharada ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin da yake tattaunawa a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels.

A cewarsa, APC ta rasa magoya baya a jihar Kano, wacce ke daga cikin jahohin da ke da yawan masu kada kuri’a a Najeriya, lamarin da ya sa suka fara neman hanyar jawo Kwankwaso da magoya bayansa na Kwankwasiyya.

Yusuf Sharada ya ce “Sun dade suna lallabar Sanata Kwankwaso da ya dawo APC saboda sanin irin karbuwarsa da dumbin magoya baya da yake da su. Hakika wannan wata dabarar siyasa ce tasu,”.

Ya kara da cewa, “Sanata Kwankwaso ya kaurace wa APC ne saboda yadda suke tafiyar da gwamnati, ya banbanta da manufofinsa. Duk da haka, suna ta matsa masa domin ya dawo ya tafi tare da su. Siyasa  lissafi ce; sun san yana da yawan magoya baya musamman daga Kano da sauran yankin Arewa maso Yamma.”

Sharada ya kuma danganta murabus din tsohon abokin hamayyar Kwankwaso a siyasa, Abdullahi Ganduje, daga kujerar Shugaban jam’iyyar APC na kasa a matsayin wata makarkashiya ta jam’iyyar domin jawo Kwankwaso daga NNPP.

“Watakila APC ta kammala shirye-shiryenta. Suna neman yawan magoya baya ne saboda tsarin manufofinsu sun cutar da talakawa; jama’a sun fara kaurace musu. Don haka, suna bukatar mutum kamar Kwankwaso wanda talakawa ke da kyakkyawar fata a kansa don su kara samun kuri’u musamman daga wannan yanki na kasar,” in ji shi.

Sharada, wanda shi ke jarorantar kungiyar Project Save Nigeria, ya ce magoya bayan Kwankwaso – wato mambobin tafiyar Kwankwasiyya – na jiran umarninsa kan jam’iyyar da za su mara wa baya a zaben shugaban kasa na 2027.

Previous Post Next Post