Tsohon Mataimakin shugaban Kasa kuma ɗan takarar Shugaban Kasa a Jam'iyyar PDP a zaben shekara ta 2023, Atiku Abubakar, da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, na daga cikin fitattun ‘yan siyasa da ke cikin wata ganawar sirri.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan taron wani bangare ne na tuntubar juna kafin a kaddamar da wani sabon dandamalin siyasa da za ta haɗa jam’iyyun hamayya gabanin zaben 2027.
Sauran da suka halarci taron sun hada da tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, da tsoffin gwamnoni Aminu Tambuwal (Sokoto), Liyel Imoke (Cross River), Babangida Aliyu (Niger) da Sam Egwu (Ebonyi).
Bayanai sun bayyana cewa David Mark ne ke jagorantar zaman, kuma tattaunawar ta mayar da hankali kan matsayar jagororin PDP na ko za su ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar, ko kuma su hade gaba ɗaya da sabon kawancen siyasa mai shirin yin hamayya da Jam'iyyar APC a zaben 2027.