A kalla mutane 36 ne aka tabbatar mutuwatrsu bayan wata fashewa mai karfi da ta haddasa gobara a wani kamfanin harhaɗa magunguna da ke jihar Telangana a kudancin kasar Indiya.
Ministan Lafiya da walwalar Jama’a na jihar Telangana, Damodar Raja Narasimha, ya bayyana cewa: “Halin da gawarwakin ke ciki na rashin gane su ya tilasta mu dauko kwararrun likitoci domin gudanar da gwajin DNA.”
An riga an kafa wani kwamiti na gwamnati domin bincikar musabbabin wannan mummunan hadari.
Fashewar ta auku ne a Litinin ɗin nan a wani bangare na masana’antar Sigachi Industries, musamman a sashen spray dryer, wanda ake amfani da shi wajen canza albarkatun kasa zuwa garin magani. Masana’antar na dab da garin Hyderabad, babban birnin jihar, kimanin kilomita 50 (mil 31).
Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Telangana, GV Narayana Rao, ya tabbatar da cewa an gano gawarwakin mutane 34 daga cikin baraguzan gine-ginen da suka ruguje, yayin da karin ma’aikata biyu suka rasu a asibiti sakamakon raunukan da suka samu.
GV Narayana Rao, ya ce“Gaba ɗaya ginin ya rushe. Mun shawo kan gobarar amma har yanzu muna ci gaba da tono a cikin baraguzan domin tabbatar da cewa babu sauran waɗanɗa suka makale,” kamar yadda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press.
Jami’in kula da harkokin mulki na yankin, P Pravinya, ya bayyana cewa mutane 25 daga cikin mamatan har yanzu ba a tantance su ba.
A halin yanzu, fiye da ma’aikata 36 na kwance a asibiti suna jinya sakamakon konewa da sauran raunuka. Rundunar ‘yan sanda ta ce fiye da ma’aikata 140 ne ke aiki a cikin masana’antar a lokacin da lamarin ya faru.
Wasu mazauna yankin sun ce sun ji karar fashewar daga nesa.
