APC Ta Nada Prof. Nentawe Yilwatda a Matsayin Sabon Shugaban ta na Ƙasa

 Jam’iyyar APC ta tabbatar da nadin Ministan Harkokin Jinƙai, Profesa Nentawe Yilwatda, a matsayin sabon Shugaban jam'iyyar na  Ƙasa.



Nadin Yilwatda ya tabbata ne a yayin taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da jam’iyyar ta gudanar a ranar Alhamis, inda aka tabbatar da shi a matsayin wanda zai jagoranci APC a matakin ƙasa.

Yilwatda ya maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya sauka daga mukaminsa a watan da ya gabata, yana mai bayyana matsalolin lafiya a matsayin dalilin murabus dinsa.

Bayan saukar Ganduje, Ali Bukar Dalori, wanda ke rike da mukamin Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Arewa, ya karɓi shugabanci na wucin-gadi. Da dama daga cikin ‘yan jam’iyya na fatan a tabbatar da Dalori a matsayin shugaban riko har zuwa  wa’adin lokacin shirya babban taron ta na ƙasa.

Sai dai NEC ta yanke shawarar mika ragamar jam’iyyar kai tsaye ga Prof. Yilwatda, wanda yanzu zai jagoranci APC zuwa sabon mataki na sake tsari da ƙarfafa tushenta kafin babban taro na da za a gudanar da zaɓe.

Nadin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar manyan ƙalubale da gyare-gyaren a cikin gida da wajen jam’iyya.

Previous Post Next Post