Jama’a Sun Tsere Daga Kauyukan su Saboda Tsoron Ramuwar Gayya, Bayan Sojoji Sun Kashe ƴan Bindiga Biyu a Zamfara

Aƙalla wasu mutane biyu da ake zargin ƴan bindiga ne sun mutu a wani samame da jami’an tsaro suka kai a ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara, lamarin da ya tayar da hankulan jama’a tare da haddasa barin kauyuka da dama saboda tsoron ramuwar gayya daga ‘yan ta’addan da suka rage.



A cewar majiya daga hukumar tsaro, harin ya auku ne a ranar 22 ga watan Yuli, lokacin da wasu masu mafarauta daga garin Mada yiwa ƴan bindigar kofar rago a tsakanin kauyukan Fegin Mahe, Chuna, Kanawa da Gundumau.

Majiyar ta bayyana wa manema labarai cewa wannan kwanton-bauna ya yi sanadin hallaka ƴan bindiga biyu, abin da ya sa fargaba ta mamaye mazauna kauyukan da abin ya shafa. Da dama daga cikinsu sun tsere zuwa garin Mada domin neman mafaka, yayin da wasu suka garzaya zuwa Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau domin zanga-zangar neman kariya daga harin ramuwar gayya.

Masu zanga-zangar sun riƙe alluna da ke ɗauke da bukatun gaggawa ga gwamnati da kuma kiran a ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin.

A martaninsa kan lamarin, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara a  ganawarsa da shugabannin al’ummar da abin ya shafa,  ya tabbatar da cewa rundunar zata ɗauki matakan gaggawa don tabbatar da zaman lafiya.

Ya kuma bayar da umarnin cewa a raka dagatan garuruwan da abin ya shafa da motar kariya ta soji (APC) a matsayin matakin wucin gadi, kafin a kammala tura haɗaɗɗiyar rundunar tsaro zuwa yankin.

Hukumar tsaro ta ce an samu daidaito a halin yanzu, kuma suna ci gaba da sa ido sosai kan lamarin.

Previous Post Next Post