Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa da Tubalin Kasa a Gumel

Rundunar ‘Yan Sandan  Jigawa ta tabbatar da kama wani matashi da ake zargi da kashe mahaifiyarsa a unguwar Dantanoma da ke karamar hukumar Gumel.



Wannan mummunan lamari ya faru ne a daren Lahadi, 29 ga Yuni, 2025, da misalin ƙarfe takwas na dare, inda ake zargin Hussaini Abubakar, mai shekaru 30, ya hallaka mahaifiyarsa Dahara Mu’azu, mai shekaru 75, ta hanyar dukan kanta da tubalin kasa.

Bayan samun kiran gaggawa, jami’an ‘yan sanda daga shelkwatar rundunar da ke  Gumel sun isa wurin, inda suka tarar da Dattijiwar cikin jini da munanan raunuka a kai. An garzaya da ita Asibitin Kwararru na Gumel, likitan da ke kan aiki ya tabbatar da rasuwarta.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar ya ce an kama wanda ake zargin, kuma yana tsare a hannun ‘yan sanda yana taimakawa wajen gudanar da bincike. 

Ana sa ran gurfanar da shi a gaban kotu da zaran an kammala binciken .

A cewar Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, CP AT Abdullahi, wannan kisa abin tada hankali ne, Ya umarci Sashen Bincike na Musamman (CID) da su ci gaba da bincike 

Rundunar ‘yan sanda ta kuma shawarci jama’a da su rika kai rahoton duk wani al'amar mai kama da  tabin hankali ko tashin hankali a gidaje ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa koga shugabannin al’umma, domin kaucewa faruwar irin wannan tashin hankali.

rundunar ta tabbatar da kudurinta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar Jigawa.

Previous Post Next Post