A cikin wani bayani mai sosa rai da aka watsa a shirin talabijin na Arewa24, tsohuwar ma’aikaciyar BBC, Halima Umar Sale, ta bayyana irin tsangwama da wariya da ta ce ta sha fama da su yayin da take aiki a gidan rediyon BBC Hausa.
A cewar Halima, lokacin da take bakin aiki, ta fuskanci matsin lamba, kyama da cin mutunci, wanda har ya kai ta ga barin aikin. Ta bayyana cewa tsawon lokaci addu'ar Allah ya sauya mata da mafi alheri.
Lamarin ya janyo martani da ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, musamman a dandalin sada zumunta, inda mutane ke bayyana damuwa kan abin da ke faruwa a wasu manyan cibiyoyin watsa labarai da ma’aikatan su mata ke fuskanta na matsin lamba.
Wannan ba shine karo na farko da irin wannan zargi ke tasowa ba. A wasu shekarun baya, ɗaya daga cikin wakilan BBC a Arewa, ya wallafa rubuce-rubuce a shafin Facebook yana bayyana irin abubuwan da suka faru da shi, ciki har da cin moriyar ganga a ya da kauranta.
Sai dai har yanzu babu wata sanarwa kai tsaye daga BBC dangane da zarge-zargen da ke sake kunno kai. Amma masana harkar aiki da kare haƙƙin ma’aikata na cewa yana da matuƙar muhimmanci a yi bitar irin waɗannan korafe-korafe da kulawa da lafiyar ma’aikata, musamman mata.
Wannan lamari ya sake buɗe tambayoyi masu nauyi: A ina dokokin kariya da adalci ke tsayawa a irin waɗannan manyan cibiyoyi? Kuma me ya kamata a yi domin kariya ga waɗanda ke fuskantar irin wannan matsin lamba?