Dakarun sojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a ci gaba da yaki da ƴan bindiga a jihar Neja, inda suka kashe da dama daga cikin su a wani artabu da ya faru a kauyen Warari, da ke karamar hukumar Rijau.
‘Yan Sanda sun ce abin ya faru ne a Kontagora, kuma harin ya auku ne a ranar 22 ga Yuli, da misalin karfe 7:20 na yamma, inda sojoji suka yi wa ƴan bindigar kwanton-bauna a wani ɓangare da ake yawan fama da hare-hare.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ƴan bindigar da aka yi arangama da su na daga cikin wata ƙungiya da ta addabi sassan Neja da Kebbi, kuma an kai musu hari ne cikin tsari na haɗin gwiwa.
“Ƴan bindiga da dama an hallaka su a lokacin artabu. Dakarunmu sun samu babbar nasara,” in ji wata majiya tsaro.
Sai dai, rahoton ya tabbatar da cewa wani soja ɗaya ya rasa ransa a yayin fafatawar.
Bayan harin, jami’an tsaro na cikin shirin ko ta kwana (red alert) domin hana harin ramuwar gayya da kuma ci gaba da gudanar da bincike da ma sintiri domin kamo wadanda suka tsere daga wurin.
Rundunar soji ta ce za ta ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri da ƙarfafa matakan tsaro a yankin domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.