Iran Ta Dakatar da Hulɗa da Hukumar Nukiliya ta MDD Bayan Hare-Haren Isra’ila da Amurka

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya rattaba hannu kan dokar dakatar da hulɗa da Hukumar Kula da Makaman Nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IAEA), a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar tashin rashin jituwa tsakanin Tehran da hukumar.



Tashar talabijin ta gwamnati ta Iran ce ta sanar da hakan a ranar Laraba, tana mai cewa shugaban ya amince da dokar dakatarwar da majalisar dokokin ƙasar ta amince da ita mako guda da ya gabata.

Wannan mataki na zuwa ne bayan hare-haren bazata da Isra’ila ta kai kan wuraren nukiliyar Iran a ranar 13 ga Yuni, da kuma hare-haren da Amurka ta sake kai wa, lamarin da ya tayar da kura tsakanin Iran da ƙasashen yamma.

A cewar sabuwar dokar, ba za a sake bai wa jami’an IAEA damar ziyartar wuraren nukiliyar Iran ba sai da izinin Kwamitin Tsaro na Ƙasa.

A martanin da ya biyo bayan wannan mataki, Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Gideon Saar, ya bukaci ƙasashen Turai masu hannu a yarjejeniyar nukiliyar ta 2015 da su karkade  “snapback” domin dawo da dukkannin takunkuman Majalisar Ɗinkin Duniya kan Iran. Wannan tsarin na snapback dai yana kan hanyar ƙarewa a watan Oktoba.

Tun bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar a shekarar 2018, Iran ta fara janye wasu daga cikin muhimman sharuddan da aka sanya mata.

A nata bangaren, gwamnatin Kasar Jamus ta bayyana cewa matakin na Iran ya aika da “wani muhimmin sakon”, yayin da kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ya jaddada cewa wajibi ne Iran ta ci gaba da aiki  da IAEA domin samun mafita ta diflomasiyya.

A nata bangaren, hukumar IAEA ta ce tana jiran karin bayani daga hukumomin Iran kan sabon matakin.

Previous Post Next Post