Rundunar Tsaro Ta Kama ’Yan Kungiyar Konyo 14 a Katsina-Ala

Rundunar tsaro ta haɗin gwiwa ta kama mutum 25 yayin wani samame a ƙaramar hukumar Katsina-Ala, Jihar Benue, inda aka tabbatar cewa 14 daga cikinsu mabiyan fitaccen jagoran ’yan ta’addan nan ne mai amfani da miyagun makamai, Konyo.



An cafke waɗannan mutane ne a ranar Litinin, yayin sintirin dawo da tsaro da tabbatar da zaman lafiya da aka gudanar a kan hanyar Katsina-Ala zuwa Takum, biyo bayan rahotannin sirri na shirin kai hari a garin Tor-Donga.

Rahotanni sun nuna cewa waɗannan mutane na cikin wata ƙungiyar masu amfani da miyagun makamai da ke da hannu wajen aikata laifukan garkuwa da mutane da kai farmaki a Gbise da ƙauyukan da ke kewaye da shi.

Sunayen waɗanda aka tabbatar da cewa mabiyan Konyo ne sun haɗa da: Awuhe Terungwa, Asawa Terseer, Terkura Audu, Terseer Gusa, Sesugh Terver, Dengba Tersugh Benjamin, Goji Abraham, Joshua Ioraenyi, Chia Fanen, Mson Iorfa, Terhemen Yanmeer, Yerfa Iorchir, Viashima Ngutor, da Vendaga Anthony — duka ’yan asalin Gbise.

An yi nasarar cafke su ne bayan dakarun haɗin gwiwa sun yi gaggawar mamaye yankin bayan gano wasu mutane da aka fara zargi a gefen hanya. Hakan tasa aka gudanar da wani samame a dajin kusa inda aka cafke ragowar mutanen da ke ƙoƙarin haɗa kansu.

Hukumomin tsaro sun ce an ƙara kaimi wajen sintiri da sa ido domin hana sake barkewar tashin hankali a yankin.

Previous Post Next Post