Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Asusun Tallafa Wa Wadanda Iftila’i Ya Shafa

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta kafa wani asusu na musamman domin tallafa wa al’umma, musamman wadanda suka fuskanci iftila’i a fadin jihar.



Kwamishinan Ma’aikatar Jin Kai da Rage Radadi, Adamu Aliyu, ne ya bayyana haka yayin taron bita na yini ɗaya da aka gudanar. Ya ce za a kafa kwamitin amintattu tare da nada darakta janar domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen gudanar da ayyukan tallafi.

Ya kara da cewa tsarin zai samar da rumbunan ajiye kayan agaji a masarautu hudu da ke jihar da kuma shiyoyi uku na jihar, domin saukaka isar da agaji cikin gaggawa.

Mai ba da shawara kan harkokin cigaba a hukumar, Dr. Aminu Magashi Garba, ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa girman jihar da yawan jama’a na bukatar irin wannan tsari don inganta bada tallafi cikin lokaci ga wadanda abin ya shafa.

Previous Post Next Post