Daga, Ado Farin Gida
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da makarantar horas da jami’an hukumar da ke kula da kare farar hula da kayayyakin gwamnati a Jihar Kano, karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
A yayin mika ginin bayan kammala shi, Shugaban Hukumar Hadeja Jama’are, Rabi’u Sulaiman Bichi, wanda ya samu wakilcin Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso, ya tabbatar da ingancin ginin tare da bayyana cewa makarantar za ta taimaka wajen bunkasa tsaro da ci gaban yankin Gwarzo.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, wanda ya samu wakilcin Kwamishina a Majalisar, Yusuf Tabuka, ya jaddada cewa yanzu ginin ya koma hannun hukumar da za ta ci gaba da gina karin gine-gine nan gaba kadan domin inganta cibiyar.
A ƙarshe, Shugaban Rundunar Civil Defence na Jihar Kano, Shafi’u Abdulmumin Dayi, ya yaba da wannan gudummawa, yana mai cewa al’ummar Kano da ma Najeriya baki ɗaya za su amfana da wannan gagarumin aiki.