Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta gargadi mazauna yankunan da ke bakin Kogin Neja da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon karuwar ruwan kogin a ɓangaren ƙasar Benin, wanda ka iya haifar da ambaliya a wasu sassan Najeriya.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Juma’a, ta umarci dukkan ofisoshinta da ke kusa da waɗannan garuruwa da su ƙara wayar da kan jama’a tare da samar da tsare-tsare na gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi.
Hukumar ta kuma shawarci mazauna yankunan da su yi la’akari da komawa wuraren da suke da kan tudu domin zama cikin aminci.
NEMA ta bukaci gwamnatocin jihohi da su yi tanadin da ya kamata tare da haɗa kai da kwamitocin ba da agajin gaggawa na kananan hukumomi don dakile illolin ambaliya idan ta faru.