Ƙungiyar Dattawan Arewa ta Nemi Haɗin Kan Gwamnoni da ‘Yan Majalisa Don Farfado da Martabar Arewa

Kungiyar Dattawan Arewa ta nemi haɗin kan gwamnonin Arewa da ‘yan majalisar tarayya domin farfado da martabar yankin Arewacin Najeriya, tare da magance matsalolin tsaro da rashin aikin yi da ke addabar matasa.



Shugaban amintattu na ƙungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu, ne ya bayyana haka a yayin taron masu ruwa da tsaki na kungiyar da aka gudanar a jihar Kano. Ya shawarci shugabannin siyasa a yankin su dauki matakan da suka dace domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar da suke jagoranta.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar a jihar Kano, Dr. Gwani Farauk Umar, ya ce suna fatan ganin an kawo ƙarshen matsalolin daba da shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar Kano, wanda ya ce zai taimaka wajen inganta tsaron jama’a da kuma kyautata rayuwar matasa.


Previous Post Next Post