NDLEA ta Kama Wani da Kilogiram 9 na Tabar Wiwi da Kudin ta Ya Kai Sama da Naira Miliyan 10 a Hanyar Zariya Zuwa Kano

Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na yankin Kiru, a Kano, sun cafke wani matashi mai shekaru 27 mai suna Umar Adamu Umar, daga Karamar Hukumar Fagge, Jihar Kano, dauke da kilogiram 9 na tabar wiwi (Colorado) da aka rarraba cikin fakiti 19.



An yi nasarar cafke shi ne a ranar 6 ga Agusta, 2025 a hanyar Zariya zuwa Kano yayin da yayi jigilar haramtattun kayayyakin daga Legas zuwa Kano.  Umar ya amsa cewa yana cikin harkar fataucin miyagun kwayoyi, kuma rundunar ta dade tana saka ido a kansa.

Tabar wiwin da aka kama ta  haura darajar Naira miliyan goma. Wannan kamun ya kawo babbar illa ga hada-hadar masu fataucin miyagun kwayoyi, don ya dakile wani bangare na samun kuɗaɗen shigar su, sannan ya katse hanyoyin samar da kayan da kuma yaɗa su, tare da rage kuɗaɗen da za su iya amfani da su wajen aikata wasu laifuka.

Rundunar NDLEA ƙarƙashin jagorancin ACGN A.I. Ahmad ta ce za ta ci gaba da ƙara himma wajen sintiri da kuma gudanar da ayyukan leken asiri don hana shigowa da miyagun kwayoyi cikin Jihar Kano.

Previous Post Next Post