Ado Danladi Farin Gida, Kano
Fiye da ‘yan daba 900 sun ajiye makaman su tare da rungumar shirin Safe Corridor da gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar domin ba su tallafi da damar komawa cikin al’umma.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci gwamnati ta tabbatar da alkawuranta na samar musu da ayyukan yi, don kaucewa komawarsu kan tsohuwar rayuwar laifi.
A nasa jawabin, Babban Kwamandan Hisba na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa hukumar za ta saka su cikin tsarin auran yar gata, tare da jan hankalin iyaye su daina la’antar ‘ya’yansu domin hakan kan jefa su cikin manyan laifuka.
Wasu daga cikin tubabbun ‘yan daban sun bayyana farin cikinsu, tare da alkawarin zama nagartattun ‘yan kasa, sabanin yadda suka kasance a baya.